LABARI: ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aikin Watanni 8

Kungiyar malaman jami’o’i wato (ASUU) ta dakatar da yajin aikinta na tsawon watanni takwas bisa sharadi.

Wani mamba a kwamitin zartarwa na kungiyar (NEC) ne ya bayyana hakan da sanyin safiyar yau Juma’a.

Kungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne a yayin wani taron shugabanninta da aka fara a daren ranar Alhamis har zuwa Juma'a.

Kungiyar ta kira taron ne domin sanin matakin da za ta dauka na gaba bayan da rassanta na Jihohin kasar suka gana kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a makon jiya.

Kotun daukaka kara ta umarci ASUU da ta dakatar da yajin aikin kafin a saurari daukaka karar da kotun masana’antu ta kasa ta yanke na umurtar malaman da su koma bakin aiki.

 Cikakkun bayanai Daga baya….

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post